Isa ga babban shafi
Najeriya-Zabe

Ina tunanin yin afuwa ga wadanda suka ci dukiyar kasa - Atiku

Tsohon Mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya bayyana cewar ya na tunanin yi wa mutanen da suka saci dukiyar kasa afuwa domin ganin sun dawo da abinda suka sata suka kuma boye a kasashen ketare.

Atiku Abubakar, dan takarar shugabancin Najeriya a Jam'iyyar PDP
Atiku Abubakar, dan takarar shugabancin Najeriya a Jam'iyyar PDP REUTERS/Tife Owolabi
Talla

Abubakar wanda shi ne dan takarar Jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa ya bayyana haka ne lokacin da ya ke amsa tambayoyi a wani shiri na musamman domin bayyana shirin da yake da shi ga al’ummar Najeriya.

Atiku Abubakar ya rike mataimakin shugaban kasa a karkashin gwamnatin Olusegun Obasanjo na shekaru 8 tsakanin shekarar 1999 zuwa shekarar 2007.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.