rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zimbabwe Emmerson Mnangagwa Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasashen Turai ke haddasa fitina a Zimbabwe - Mnangagwa

media
Shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa. ZINYANGE AUNTONY / AFP

Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya zargi kasashen yammacin Turai da goyon bayan boren da dubban ‘yan kasar suka yi, cikin watan Janairu, a dalilin karin farashin man fetur.


Yayin zantawa da manema labarai a birnin Harare, Mnangagwa, ya ce makiyan Zimbabwe daga cikin kasashen Turan ne suke taimakawa babbar jam’iyyar adawa ta MDC da wasu kungiyoyi masu zaman kansu, wajen shirya zanga-zangar adawa da gwamnatinsa.

Akalla fararen hula 12 suka hallaka yayin zanga-zangar, bayan da jami’an tsaro suka yi amfani da karfi wajen murkushe tarzomar da ta barke a wasu biranen kasar ta Zuimbabwe, musamman a Harare da Bulawayo, abinda ya kai ga satar kayayyaki daga shaguna, hadi da cinna musu wuta.

Sai dai kasashen Amurka da Birtaniya, da kuma kungiyar taryyar turai EU, sun soki gwamnatin Manangagwa, bayan da jami’an tsaro suka kama sama da mutane 1000, daga bangaren ‘yan adawa, da sauran mutane ciki har da kananan yara.