rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Maiduguri BOKO HARAM Kamaru

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan gudun hijirar Najeriya dubu 35 sun samu mafaka a Kamaru

media
Wasu 'yan Najeriya da rikicin Boko Haram ya tilastawa tserewa zuwa Kamaru. IRIN News/Monde Kingsley Nfor

Majalisar Dinkin Duniya tace yanzu haka yan gudun hijirar Najeriya dubu 35 da suka nemi mafaka a kasar Kamaru sakamakon harin da mayakan boko haram suka kai garin Rann na cikin koshin lafiya.


Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar, tace sai dai wasu daga cikin wadanda suka samu mafaka a Kamaru na jefa kansu cikin hadari saboda yadda suke takawa da kafa domin komawa garin na Rann.

Jami’in Majalisar dake Kamaru, Allegra Baiocchi, yace ya ga mutane da dama dake zama cikin fargaba a cikin 'yan gudun hijirar saboda yadda aka lalata rayuwar su.

Shi kuwa Geert de Casteele, jami’in hukumar kula da 'yan gudun hijira a kasar ya yaba ne da daukin da kungiyoyin agaji suka kaiwa bakin.