rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Cote d'Ivoire

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

kotun duniya ICC ta sallami tsohon shugaban Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo bisa sharadi

media
Laurent Gbagbo, tsohon shugaban cote d'ivoire a lokacin a kotun CPI, 15 janairu 2019. CPI

Kotun ICC dake shariar masu aikata laifukan yaki ta saki tsohon shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo, dan shekaru 73 dake tsare hannunta, bayan wanke shi da ta yi daga laifukan da ake zarginsa da aikatawa na cin zarafin dan adam a rikicin zaben kasar na 2010-2011 da ya sarwantar da rayukan jama’a sama da dubu 3.


Sai dai kuma a karkashin saki kotun ta gindaya wa Gbagbo sharudda kuma zai kasance a Belgium har sai bayan daukaka kara da ake jin masu gabatar da kara za su daukaka.

Cikin sharuddan aka giundaya masa akwai na bukatar ya kai kansa kotun idan an neme shi, kuma zai ajiye passpo dinsa.

Ya kasance na farko tsohon shugaban wata kasa dakotun ta garkame shi tun shekara ta 2011, bayan da ya yi kememe ya ki sauka daga mulki bayan ya fadi zabe, har sai da aka zubar da jinni a kasar.