rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kamaru Hakkin Dan Adam Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka ta katse tallafin da take baiwa Kamaru

media
Wasu dakarun rundunar sojin kasar Kamaru. REUTERS/Joe Penney

Amurka ta sanar da katse tallafin tsaron da take baiwa Kamaru saboda abinda ta kira take hakkin Bil Adama da jami’an tsaron kasar ke yi.


Ma’aikatar cikin gidan Amurka ta kara da cewa, za ta dakatar da shirin mikawa Kamaru tankunan yaki saboda rashin gamsuwa da rawar da jami’an tsaron ta ke takawa.

Matakin na Amurka ya zo ne a daidai lokacin da wasu kungiyoyin kare hakkin Bil Adama 15, suka bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta kaddamar da bincike kan yadda Gwamnatin Kamaru ke take hakkin Dan Adam a yankin da ake amfani da Turancin Ingilishi.

Cikin kungiyoyin da suka sanya hannu kan takardar korafin sun hada da Civicus da Cibiyar kare hakkin Bil Adama da Dimokiradiya a Afirka, wadanda suka zargi gwamnatin Kamaru da bada umarnin kai hare-haren soji kan mutanen yankin.

Wasikar kungiyoyin ta bukaci gudanar da sahihin bincike cikin gaggawa kan lamarin.

Kungiyar ICG tace sama da jami’an tsaro 200 da fararen hula akalla 500 aka kashe a rikicin yankin na masu amfani da Turancin Ingilishi, yayin da Majalisar Dinkin Duniya tace sama da mutane 437,000 suka tsere daga yankin.