Isa ga babban shafi
Saliyo

Saliyo ta ayyana dokar ta baci kan laifin fyade

Shugaban Kasar Saliyo Julius Maada Bio ya bayyana saka dokar ta baci sakamakon cigaba da yawaitar matsalar fyade da cin zarafin kananan yara da ke faruwa a kasar, tare da hukuncin daurin rai da rai a kan duk wanda aka kama da aikata mumunar aika aikar.

Shugaban kasar Sierra Leone' Julius Maada Bio na gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya a birnin  New York, na kasar Amruka a Sept  27, 2018. REUTERS/Carlo Allegri
Shugaban kasar Sierra Leone' Julius Maada Bio na gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, na kasar Amruka a Sept 27, 2018. REUTERS/Carlo Allegri REUTERS/Carlo Allegri
Talla

Kididdigar yan sandan kasar na nuna cewa adadin wadanda aka ci zarafinsu a cikin shekarar da ta gabata ta hanyar fyade ya ninka na bara, inda adadin ya kai dubu 8505, sabanin na bara da ke da dubu 4705, a fadin kasar da ke da adadin mutane miliyan 7.5

Rahotanni na nuna cewa kashi 3 cikin hudu na matsalar fyade ya shafi kananan yara. A dalilin haka ne shugaban kasar Julius Maada Bio ya kafa dokar ta baci a kasar, inda ya yi jawabi cikin wani yanayi na takaici cewa duk wanda aka kama da laifi zai yi zaman gidan yari har tsawon rayuwar shi.

Shugaban ya ce ya zama wajibi asibitoci a fadin kasar su yi duk mai yiwuwa wajen ba wadanda lamarin ya rutsa da su kulawar kyauta.

Bio ya ce za’a kafa wani sashe na yan sanda da ke kula da duk wani lamari da ya shafi cin zarafi ko fyade, hakazalika za’a kafa kotun da zata mayar da hankali wajen hukunta wadanda aka kama da aikata mumunar aika aikar.

Har ila yau shugaban ya ce za’a fidda lambar tarho na kiran gaggawa ga duk wadanda ke bukata.

A cewar Rainbow Initiative wata cibiya da ke yiwa wadanda aka ci zarafinsu kulawar kyauta, daga cikin mata da yara dubu 30 da aka taba yi wa fyade a kasar, kashi 93 cikin 100 na kasa da shekara 17 da haihuwa.

Da dama daga cikin wadannan aka ci zarafinsu sun kamu da cutuka kamar HIV, yayin da daruruwa daga cikin su sun samu juna biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.