rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ghana Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan sanda sun kama mutane 6 bisa zarginsu da kisan dan Jarida

media
Ahmed Hussein-Suale, dan jaridar da wasu 'yan bindiga suka hallaka. Hussein-Suale Family/Handout/REUTERS

Yan sanda a kasar Ghana sun ce sun kama mutane 6 da ake zargi da hannu wajen kisan gillar da aka yiwa wani dan jarida mai bincike Ahmed Hussein-Suale, wanda ya taimaka wajen bankado cin hancin da ya mamaye hukumar kwallon kafar kasar.


Kakakin rundunar ‘yan sandan kasar ta Ghana David Eklu yace an bada belin wadanda ake zargin bayan yi musu tambayoyi.

Eklu yace cikin wadanda aka yiwa tambayoyi harda dan majalisa kuma dan kasuwa Kennedy Agyapong.

Jami’in yace suna aiki tukuru wajen ganin an hukunta wadanda aka tabbatar da laifi akan su.