Isa ga babban shafi
Najeriya-Zabe

NOA ta yi gargadi kan yada sakamakon bogi a zabukan Najeriya

Hukumar wayar da kan jama’a ta Najeriya NOA ta bukaci ‘yan Najeriya su kauracewa yada sakamakon zabe na bogi tun kafin sanarwar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar INEC yayin manyan zabuka masu zuwa a wannan watan.

NOA ta ce babu wanda ke da alhakin sanar da sakamakon zabe face hukumar INEC don haka sanar da sakamakon tamkar yi mata katsalandan ne
NOA ta ce babu wanda ke da alhakin sanar da sakamakon zabe face hukumar INEC don haka sanar da sakamakon tamkar yi mata katsalandan ne AFP/Pius Utomi Ekpei
Talla

Shugabar hukumar reshen jihar Gombe a arewacin Najeriyar Mrs Adaline Patari ta ce dole ne ‘yan kasar su kauracewa yada jita-jita musamman lokacin zabe, baya ga jiran sakamakon zaben daga hukumar da ke da alhakin tattara shi.

Da ta ke shaidawa kamfanin dillancin labaran Najeriyar NAN, Mrs Patari ta ce ta hanyar kame baki da kaucewa yada jita-jita ne za a samu nasarar gudanar da zaben cikin lumana kamar yadda ake fata.

Hukumar ta NOA ta ce babu wanda ke da alhakin sanar da sakamakon zabe face hukumar INEC don haka sanar da sakamakon tamkar yi mata katsalandan ne.

Ka zalika hukumar ta ce ta na ci gaba da wayar da kan jama’a kan yadda za su yi zaben ba tare da lalata kuri’unsu ba.

Hukumar NOA ta kuma nemi al’ummar Najeriya su kaucewa kalaman batanci tsakaninsu musamman magoya bayan mabanbantan jam’iyyun siyasa.

A bangare guda hukumar ta nemi shugabannin gargajiya da na addini su taka muhimmiyar rawa wajen jan hankulan magoya bayansu don kaucewa rikici yayin zabukan na bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.