Isa ga babban shafi
Chadi

Sojin Chadi sun yi gagarumar nasara kan 'Yan tawaye

Ma’aikatar tsaron Chadi ta tabbatar da kame ‘yan tawaye fiye da 250 ciki har da jagororinsu bayan wani sumame da ta kai kan ayarin motocinsu lokacin da su ke shirin tsallako iyakar kasar daga Libiya cikin watan Janairu.

Dakarun sojin kasar kasar Chadi
Dakarun sojin kasar kasar Chadi REUTERS/Emmanuel Braun
Talla

A sanarwar da Babban hafson sojin kasar ya fitar a yau, ya ce za su ci gaba da kai sumame maboyar ‘yan tawayen yankin Ennedi da ke gab da kan iyakar kasar da Libya da Sudan baya ga sanya tsaurarn matakan tsaro.

Sanarwar ta ce mayakan 'yan tawayen su 250 tare da jagororinsu 4 yanzu haka na hannun hukuma yayinda aka lalata motocinsu fiye da 40 a hare-haren ciki har da wadanda aka kai ta sama da jiragen yakin Faransa.

A makon jiya ma shugaban kasar Idris Deby ya sanar da cewa dakarun sojin kasar sun yi gagarumar nasara kan 'yan tawayen da ke kaddamar da hare-hare a kasar.

Chadi wadda ke cikin kasashen G5 Sahel da ke fuskantar hare-haren ta'addanci ko a bara ta fuskanci hare-haren 'yan tawayen matakin da ya tilasta mata daura damarar yakarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.