Isa ga babban shafi
Algeria

Zan sake tsayawa takara- Bouteflika

Shugaban Algeria, Abdelaziz Bouteflika mai shekaru 81 da haihuwa ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar zabe karo na 5 a watan Afrilu mai zuwa.

Abdelaziz Bouteflika akan keken marasa lafiya
Abdelaziz Bouteflika akan keken marasa lafiya RYAD KRAMDI / AFP
Talla

Shugaban da ke fama da rashin lafiya ya bayyana haka ne a wani sakonsa da aka watsa a kafafen yada labaran gwamnatin kasar bayan ya samu goyon bayan daga jam’iyyarsa.

Bouteflika da ya gamu da rashin lafiya sakamakon bugun zuciya, ya rage yawan bayyana a bainal jama’a da kuma gudanar da harkokin gwamnati kamar yadda aka saba.

Har yanzu al’ummar Algeria na mutunta Bouteflika saboda rawar da ya taka wajen kawo karshen yakin basasar kasar da aka kwashe tsawon shekaru ana fama da shi, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla dubu 200.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin bil’adama da ‘yan adawa na caccakar sa sbaoda yadda yake gudanar da mulkin kama-karya a cewarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.