Isa ga babban shafi
Najeriya-Zabe

Gobara ta sake kone Ofishin hukumar INEC a Najeriya

Dai dai lokacin da ya rage kwanaki 4 a gudanar da babban zaben Najeriya, wata sabuwar gobara ta sake kone shalkwatar hukumar zaben kasar INEC da birnin Awka a jihar Anambra.

Wannan dai ne karo na 3 da gobarar ke kone manyan Ofisoshin hukumar zaben ta INEC a Najeriya dai dai lokacin da zabe ke sake karatowa
Wannan dai ne karo na 3 da gobarar ke kone manyan Ofisoshin hukumar zaben ta INEC a Najeriya dai dai lokacin da zabe ke sake karatowa NAN
Talla

Gobarar wadda ta cinye dakunan adana na’urar tantance masu kada kuri’a na zuwa ne kwanaki biyu bayan makamanciyarta a jihar Pulato, kari kuma akan wata da ta faru a Ofishin hukumar ta INEC a Abia.

Kamfanin dillancin labaran Najeriyar NAN ya ruwaito cewa har zuwa lokacin da ya ke wallafa rahoton jami’an kashe gobara basu ci karfin wutar da ta tashin ba.

Rahotanni sun ce tuni aka aike da jami’an Civil Defence dana DSS da kuma ‘yan sanda don tabbatar da tsaron wurin.

Nkwachukwu Orji, kwamishinan zaben na jihar the Anambra, ya ce ba su gama tantance asarar da gobarar ta tafka ba.

Sai dai ya tabbatar da cewa gobarar ta shafi na’urar tantance masu kada kuri’ar da aka fi sani da Card Reader wadda aka shirya amfani da ita a babban zaben Najeriyar mai zuwa na ranar 16 ga watan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.