rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Habasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Maganin amfanin gona na kashe mutane dubu 400 kowacce shekara

media
Bayanan masanan sun bayyana cewa duk mutum 10 cikin 100 na mutuwa sanadiyyar magungunan da ake sanyawa kayakin abinci a sassan duniya Reuters

Masana daga kasashen duniya 125 tare da manyan jami’an gwamnati yanzu haka sun fara wani taro a Addis Ababa na kasar Habasha don tattauna yadda za a kaucewa amfani da magunguna a kayan abincin wadanda ke kashe mutane sama da dubu 400 kowacce shekara.


Taron wanda ke gudana a karkashin Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya da kuma Hukumar kula da Lafiya ya samu halartar jami’an gwamnati da masana harkar noma da kuma sarrafa abinci.

Shugaban hukumar samar da abinci Jose Graziano Da Silva ya bayyana cewar  duniya ana samar da abincin da kowa zai ci, amma kuma akasarin abincin na dauke da guba.

Shima babban jami’in Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da ingancin abinci, Kazuaki Miyagishima ya ce binciken su ya nuna cewar mutum guda daga cikin mutane 10 na kamuwa da rashin lafiya sakamakon cin abincin da ke dauke da guba.

Alkaluman hukumar sun ce daga cikin mutane miliyan 600 dake cin abincin dake dauke da irin wadannan sinadarai masu guba, 420,000 ke mutuwa kowacce shekara, kuma kashi 40 daga cikin su yara ne kanana.

Hukumar ta ce ana danganta irin wadannan rashin lafiyar ne da abinci maimako wasu cututtuka da suka hada da amai da gudawa zuwa kansa.

A na shi sakon, shugaban gudanarwar kungiyar kasashen Afirka Moussa Faki ya bayyana cewar ingancin abinci na da muhimmanci ga kowanne Bil Adama, yayin da Afirka ke fama da wannan matsalar.

Shugaban hukumar lafiya ta duniya, Tedros Adahanin Gebreyesus ya ce ana danganta tsaftar abinci da cigaba ta hanyoyi daban daban.