Isa ga babban shafi
Najeriya

Yan takarar zaben Najeriya sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

Yan takarar shugaban kasar Najeriya a zaben da za’ayi a karshen wanan mako sun sanya hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiyar da kungiyar zaman lafiya ta tsohon shugaban kasa Abdusalami Abubakar ta jagoranta.

Yan takara a zaben Shugabancin Najeriya
Yan takara a zaben Shugabancin Najeriya Femi Adeshina
Talla

Bikin sanya hannu ya samu halartar mutane da dama cikin su harda tsohon shugaban kasa Janar Yakubu Gowon da shugaban hukumar zabe Frafesa Mahmud Yakubu da Sarakunan gargajiya da kuma masu sa ido daga ciki da wajen Najeriya.

Yan takarar zaben sun janyo hankalin magoya bayan su da su kaucewa daukar duk wani mataki da zai haifar da tashin hankalin lokacin zaben da kuma bayan sa.

Dan takarar Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya roki shugaba Muhammadu Buhari da ya tabbatar da cewar an kirga duk wata kuri’ar da aka kada domin baiwa kowa damar ganin kuri’ar sa tayi tasiri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.