rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Kaduna

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Adadin wadanda 'yan bindiga suka kashe a Kaduna ya kai 130- El-Rufa'i

media
Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El Rufa'i NAN

A Najeriya Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufa’I ya tabbatar da karuwar adadin mutanen da suka mutu a karamar hukumar Kajuru na jihar zuwa 130. A cewar El-Rufa'i yanzu haka ana ci gaba da lalubo wadanda ke da hannu a kashe-kashen kuma nan gaba kadan za a mika su gaban hukuma.


Kisan, wanda kawo yanzu ba a tabbatar da wadanda suka aikata shi ba, a juma’ar da ta gabata gwamnan ya sanar da kisan mutane 66 yayinda rundunar sojin kasar ta tabbatar da hakan daga bisani.

A jawabansa ga manema labarai, bayan kammala taron masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro da shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya kira, El-Rufa’I ya ce an dauki matakan lalubo masu hannu a kasha-kashen tare da hukunta su.

Yayin taron kan sha’anin tsaro, wanda ya samu halartar gwamnonin jihohin Najeriya 3 da manyan hafoshin sojin kasar da ma sauran shugabannin hukumomin tsaro, Muhammadu Buhari ya nemi samar da mafita ga rashin tsaron jihohin Borno, Yobe Kaduna da kuma jihar Adamawa.

Tuni dai kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Kaduna Ahmad Abdulrahman wanda shi ma ya halarci taron karkashin jagorancin shugaban Najeriyar, ya sanar da kame wasu mutane 8 wadanda ya ce suna da hannu a kasha-kashen na ranar juma’ar da ta gabata.