rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Sudan ta Kudu Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sojojin Sudan ta kudu sun yi wa mata fiye da 100 fyade - rahoto

media
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Sudan STRINGER / AFP

Wani rahotan binciken Majalisar Dinkin Duniya ya zargi sojojin gwamnatin Sudan ta kudu da yiwa mata da ‘yam mata sama da 100 fyade a garin Bentiu dake arewacin kasar. A farkon watan Disambar bara, hukumomin Majalisar Dinkin Duniya 3 sun bada rahotan cewar mata da yan mata sama da 150 suka fito fili suka bayyana cewar an yi musu fyade a cikin kwanaki 12, inda suka bukaci taimako kan azabar da suka fuskanta.


Rahotanni sun ce wadanda suka aikata aika aikan na dauke da makamai, kuma wasu daga cikin su na sanye da kayan soji.

Hukumar kare hakkin Bil Adama ta Majalisar tace sun samu shaidar dake nuna cewar sojoji ne suka aikata laifin.

Sai dai rahotan yace babu shaidar dake nuna cewar kwamandodjin sojin ne suka bada umurnin aikata laifin.