rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Ghana

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Martanin Najeriya dangane da korar da Ghana ta yiwa wasu yan kasar

media
Taswirar yankin yammacin Afrika RFI

Jakadan Nigeria a Ghana Michael Abikoye ya nuna rashin jin dadin Najeriya game da korar ‘yan Najeriya 723 da Ghana tayi tsakanin shekarar da ta gabata zuwa wannan lokaci.


Jakadan Nigeria a Ghana Michael Abikoye ya

fadawa wani taro da yayi da jami’an hukumar kula da shige da fice na Ghana cewa abin babu dadi ko kadan.

Ya ce ‘yan Nigeria 81 aka kora a watan jiya saboda zargin zanba ta yanar gizo da zarce wa’adin zama a kasar, yayinda a wannan watan aka kori mutane 115 saboda zargin karuwanci da kuma zarce wa’adin zama a kasar.