rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Uganda

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaba Museveni na Uganda na neman shugabancin kasar karo na 6

media
Shugaba Yoweri Museveni na Uganda © GAEL GRILHOT / AFP

Jam'iyyar da ke mulkin kasar Uganda ta amince da shugaba Yoweri Museveni da ya tsaya takarar shugaban kasa wa’adi na 6 a zaben da za’a gudanar a shekarar 2021.


Taron Jam’iyyar National Resistance Movement ya bukaci shugaba Museveni da ya cigaba da jagorancin kasar lokacin da manyan jami’an Jam’iyyar suka gana.

Wannan mataki na zuwa ne bayan Majalisar kasar ta amince da dokar cire shinge shekarun tsayawa takarar shugaban kasa wanda ya haramtawa mutumin da ke da shekaru 70 tsayawa zabe.

Shugaba Yoweri Museveni dai na da shekaru 71 a duniya yanzu haka.