rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Algeria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An yi arrangama tsakanin 'yan sanda da mutane a Algiers

media
Shugaban Algeria Abdelaziz Bouteflika, mai shekaru 81 da ke fama da rashin lafiyar mutuwar barin jiki. REUTERS/Zohra Bensemra

Hankula sun tashi Algiers babban birnin Algeria, sakamakon wata kazamar arrangama tsakanin jami’an tsaro da daruruwan masu zanga-zangar adawa da aniyar shugaban kasar Abdelazizi Bouteflika ta neman zarcewa bisa mulkin kasar wa’adi na 5.


‘Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar da suka yi yunkurin tunkarar shiga ginin fadar gwamnatin kasar, hakan tasa masu zanga-zangar maida martani da duwatsu, da nufin yiwa jami’an tsaro rotse.

A ranar 10 ga watan Fabarairu, shugaban na Algeria Abdelaziz Boutiflika mai shekaru 81, ya bayyana aniyar sake neman wa’adi na 5 a zaben kasar na watan Afrilu mai zuwa, bayan shafe shekaru kusan 20 yana mulkin kasar.

A shekarar 2013, shugaban na Algeria ya kamu da larurar mutuwar barin jiki, kuma tun daga waccan lokacin ba kasafai ake ganinsa a bainar jama’a ba.