rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Senegal Macky Sall

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Al'ummar Senegal na kada kuri'a a zaben shugaban kasa

media
Daya daga cikin 'yan takarar shugabancin kasar Senegal Idrissa Seck, tare da magoya bayansa. 3/02/ 2019. REUTERS/Zohra Bensemra

Yau Lahadi, al’ummar Senegal ke kada kuri’a a zaben shugabancin kasar, bayan kawo karshen yakin neman zaben ‘yan takara a ranar Juma’ar da ta gabata.


Yan takara 5 ne za su fafata a zaben shugabancin na Senegal, cikinsu har da shugaba mai ci Macky Sall, yayinda ake sa ran ‘yan kasar akalla, miliyan 6 da dubu 500 za su kada kuri’a.

Karo na farko kenan da zaben shugaban kasa zai gudana a Senegal bayan zaben raba gardama na shekarar 2016, wanda ya bada damar rage yawan shekarun da shugaba zai shafe bisa mulki daga shekaru 7 mai tsarin wa’adi daya, zuwa shekaru 5 bisa tsarin wa’adi guda biyu.

Daga cikin ‘yan takarar 5 da za su fafata, Ousmane Sonko mai shekaru 44 ne mafi kankanta a cikinsu, wanda kuma ya sha alwashin sake nazari kan kwagilolin manyan ayyuka da gwamnatin Senegal da baiwa wasu kamfanonin Faransa, muddin yayi nasarar lashe zaben.