Isa ga babban shafi
Venezuela

Maduro ya yanke alaka tsakaninsa da Colombia

Dakarun sojin Venezuela masu biyayya ga shugaba Nicolas Maduro, sun yi amfani da karfi wajen, datse yunkurin shigo da kayan agaji na abinci da magunguna da magoya bayan jagoran ‘yan adawa Juan Guaido suka yi yunkurin shigar da su kasar.

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro.
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro. REUTERS/Marco Bello
Talla

Yayin arrangamar, jami’an tsaron na Venezuela sun hallaka masu bore 2, tare da jikkata wasu da dama.

Matakin dai yasa, Juan Guaido mai samun goyon bayan kasashe 50, ciki har da Amurka da wasu manyan kasashen Turai, mika bukata ga gwamnatin Donald Trump, da cewa tana da damar yin amfani da kowace hanya wajen hambarar da gwamnatin Maduro da ya kira haramtacciya.

Tuni dai shugaba Maduro ya katse duk wata alaka da Colombia, bayan da kasar ta goyi bayan babban abokin hamayyar tasa Juan Guiado da ya ayyana kansa a matsayin halataccen shugaba.

Tsattsauran matakin na shugaba Maduro, ya biyo bayan taimakawa magoya bayan Guaido da Colombia ta yi, wajen shigo da kayayyakin agaji na magunguna da abinci da Amurka ta yi nufin shigar da su ga dubban ‘yan Venezuela da ke bukatar taimako, yunkurin da Maduro ya haramta a baya.

A halin da ake  ciki, Maduro ya baiwa jami’an diflomasiyyar Colombia sa’o’i 24 su fice daga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.