rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Senegal Macky Sall

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gwamnati ta yi ikirarin lashe zabe gabannin kidaya kuri'u

media
Shugaban kasar Senegal Macky Sall. Photo: Seyllou/AFP

Fira Ministan Senegal Mahammed Boun Abdallah Dionne ya ce shugaba Macky Sall ya lashe zaben shugabancin kasar da aka gudanar jiya lahadi, a daidai lokacin da hukumar zabe ke aikin tattara sakamakon kuri’unda aka kada a ranar Lahadi.


To sai dai biyu daga cikin ‘yan takara hudu da suka kara da shugaban a wannan zabe, wato tsohon Fira Minista Idrissa Sseck da kuma Ousmane Sanko sun ce sai an je zagaye na biyu kafin samun wanda zai lashe zaben.

Karo na farko kenan da zaben shugaban kasa zai gudana a Senegal bayan zaben raba gardama na shekarar 2016, wanda ya bada damar rage yawan shekarun da shugaba zai shafe bisa mulki daga shekaru 7 mai wa’adi daya, zuwa 5 bisa tsarin wa’adi biyu.