rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ghana

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

John Dramani Mahama zai sake tsayawa takarar shugabancin Ghana

media
Tsohon shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama AFP PHOTO / ISSOUF SANOGO

Babbar Jam’iyyar adawan Ghana ta NDC ta zabi tsohon shugaban kasar John Dramani Mahama a matsayin wanda zai mata takarar zaben shekara mai zuwa domin fafatawa da shugaba mai ci Nana Akufo-Addo.


Akufo-Addo ne ya kawar da Mahama a karagar mulki a zaben shekarar 2016, sakamakon matsalar tattalin arzikin da kasar ta fuskanta da kuma faduwar farashin man fetur da zinare wanda kasar ta dogara da su.

Kafin dai zaben shekarar 2016, Mahama wanda ya gaji shugaban kasar da ya rasu, ya kada Addo a zaben shekarar 2012.