rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Algeria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaba Abdul'aziz na Algeria na duba lafiyarsa a Switzerland

media
Shugaban kasar Algeria Abdelaziz Boutefika AFP/Eric FEFERBERG

Rahotanni daga kasar Switzerland sun ce yanzu haka ana duba lafiyar shugaban kasar Algeria Abdelaziz Bouteflika a wani asibiti da ke Switzerland a dai dai lokacin da ya ke shirin tsayawa takarar zabe a wa’adi na 5.


Kamfanin dillancin labaran Faransa ya jiyo Jaridar Tribune da ke Geneva na cewa, majiyoyi masu karfi daga asibitin da ake kula da shugaban sun tabbatar da labarin.

Shugaban mai shekaru 84 da ake turawa a keken guragu tun bayan bugun zuciyar da ya gamu da ita a shekarar 2013 ya ce a karshen wannan mako zai gabatar da takardar sake takarar sa na mukamin shugaban kasa.