Isa ga babban shafi
Algeria

'Yan sanda sun raunata masu zanga-zanga a Algeria

Jami’an tsaro sun raunata da dama daga cikin masu zanga-zangar adawa da tazarcen shugaban Algeria da ke fama da rashin lafiya, AbdelAziz Bouteflika.

Masu zanga-zangar adawa da tazarcen shugaba AbdelAziz Bouteflika
Masu zanga-zangar adawa da tazarcen shugaba AbdelAziz Bouteflika AFP Photos/Ryad Kramdi
Talla

Masu zanga-zangar sun yi arangama da jami’an ‘yan sanda da suka yi ta dukan mutane da sanduna kamar yadda wakilin Kamfani Dillancin Labaran Faransa na AFP ya rawaito.

Har ila yau, jami’an kwantar da tarzoma sun cilla hayaki mai sa kwalla da zummar tarwatsa masu zanga-zangar a wani dandali mai tazarar kilomita 1.5 daga fadar gwamnatin kasar da ke birnin Algier.

Shugaba Bouteflika na neman wa’adi na biyar ne akan karagar mulki a zaben da za a gudanar a ranar 18 ga watan Afrilu mai zuwa.

Tun a shekarar 1999, Bouteflika ya dare kan karagar mulkin Algeria, yayinda a shekarar 2013 ya gamu da rashin lafiyar shanyewar barin jiki, abinda ya sa a yanzu ake tura shi a keken marasa lafiya kuma ba kasafai yake bayyana cikin jama’a ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.