Isa ga babban shafi
Sudan

Yarjejeniyar sulhun Sudan ta kudu na daf da rushewa

Shugabannin Cocin Katolika na Sudan ta Kudu, sun yi gargadin cewa, yarjejeniyar sulhu da ta kawo karshen yakin basasar kasar mai watanni 6, na barazanar wargajewa.Shugaban mabiya darikar Katolika na kasar Archbishop Paulino Lukudu, ya ce a halin da ake ciki, dakarun sojin Sudan ta Kudu da kuma tsaffin ‘yan tawaye masu biyayya ga mataimakin shugaban kasar Riek Machar na shirye-shiryen sake afkawa juna da azababben yaki, watanni 6 bayan cimma sulhu a shekarar bara.

Salva Kiir da  Riek Machar
Salva Kiir da Riek Machar YONAS TADESSE / AFP
Talla

Yakin basasa tsakanin dakaru masu biyayya ga shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar ya soma ne a watan Disambar 2013, lokacin da Kiir ya zargi Machar da yunkurin yi masa juyin mulki. Daga bisani dai yakin ya juye zuwa na kabilanci, wanda kuma ya yi sanadin hallakar akalla ‘yan kasar dubu 400,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.