Libya: An azabtar da 'yan ci rani a sansanin karkashin kasa
Rahotanni daga Libya sun ce 'yan ci rani akalla 30 da ke son tsallakawa Turai ciki har da kananan yara, sun fuskanci azabtarwa a wani sansanin karkashin kasa, saboda yunkurin da suka yi na tserewa daga inda ake tsare da su.
Wallafawa ranar:
Akalla bakin-haure 150 ne suka balle daga sansanonin da mayaka masu iko da yankunan Libya ke tsare da su, da nufin rugawa zuwa hukumar yaki da safarar bakin-haure ta kasar.
Wani shaidar gani da ido ya ce kafin yukurin tserewa, sai da bakin-hauren suka yi zanga-zangar nuna bacin rai kan munin yanayin sansanonin da aka tsare su.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar dinkin duniya, tace mafi akasarin bakin-hauren da ake tsare dasu a Libya a yanzu, wadanda kasashen Turai suka maido kasar ne, bayan da sukai yunkurin ketara takun Mediterranean zuwa nahiyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu