rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Algeria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Alkawarin Bouteflika ya sake harzuka dubban masu zanga-zanga

media
Wasu daga cikin dubban 'yan kasar Algeria da ke zanga-zangar neman kawo karshen shugabancin AbdelAziz Bouteflik. REUTERS/Zohra Bensemra

Shugaban Algeria AbdelAziz Bouteflika yayi alkawarin sauka daga mulkin kasar bayan shekara daya, idan ‘yan kasar suka bashi damar zarcewa bisa wa’adi na 5, a zaben da za a yi ranar 18 ga watan Afrilu.


Alkawarin na Bouteflika, ya zo a dai dai lokacin da ya ke fuskantar zanga-zangar neman kawo karshen mulkinsa na tsawon shekaru 20 da dubban ‘yan kasar ke yi.

Sai dai a maimakon alkawarin na shugaba Bouteflika ya kara harzuka dubban ‘yan kasar ta Algeria ne, a maimakon kwantar musu da hankula, wadanda suka sake shirya sabuwar zanga-zanga.

A shekarar 1999 AbdelAziz Bouteflika mai shekaru 82 a yanzu, ya dare kujerar shugabancin Algeria, amma a shekarar 2013 ya rage fita cikin jama’a, bayan kamuwa da ciwon mutuwar barin jiki.

Ma’aikatar lafiyar Algeria, ta ce mutane 183 sun jikkata a zanga-zangar da dubban ‘yan kasar ke ci gaba da yi, ta adawa da tazarcen shugaba Bouteflika.