rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zaben Najeriya Kano

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotu ta dakatar da dan takarar gwamnan Kano na Jam'iyyar PDP

media
Dan takarar kujerar Gwamna a karkashin Jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf. Daily Post Nigeria

Babbar kotun jihar Kano ta dakatar da takarar Abba Kabir Yusuf da ke neman kujerar gwamnan jihar karkashin jam’iyyar PDP, bisa hujjar rashin gudanar da zaben fidda gwani.


Zaman sauraron shari’ar karkashin Alkali Ambrose Lewis a yau Litinin ya ce Jam’iyyar ta PDP ba ta fitar da Abba Kabir Yusuf a tsarin da ya dace wajen fitar da dan takara ba.

Lauyan masu shigar da kara Kabiru Usman, ya ce dole ne Jam’iyyar ta PDP ta sake tsayar da dan takara na daban gabanin zaben gwamnoni a ranar 9 ga watan nan.

Sai dai lauyan PDP, Bashir Yusuf ya ce hukuncin kai tsaye bai shafi Abba Kabir Yusuf ba, face jam’iyyar ta PDP wadda ke da zaben sake gudanar da zaben fidda gwani.

A cewar Bashir Yusuf, Jam'iyyar ta PDP za ta bi umarnin Kotu don tabbatar da nasararta a zabe mai zuwa.

Hukuncin na Kotu dai na da nasaba da karar da Ali Amin Little ya shigar gaban kotun wanda ya ke kalubalantar matakin da Jam'iyyar ta bi wajen fitar da dan takarar gwamnan a jihar Kano.