rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Algeria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Lauyoyi sun bi sahun masu zanga-zanga a Algeria

media
Dubun dubatar al'ummar Algeria kenan da ke ci gaba da zanga-zangar adawa da takarar shugaba Abdelaziz Bouteflika karo na 5 duk da rashin lafiyar da ya ke fama da ita REUTERS/Zohra Bensemra

Lauyoyi a kasar Algeria sun bi sahun sauran jama’ar kasar wajen gudanar da zanga zangar adawa da takarar shugaban kasa Abdelaziz Bouteflika wanda ke neman wa’adi na 5 duk da rashin lafiyar da ya ke fama da ita da kuma shekaru.


Masu zanga zangar sun yi tattaki zuwa kotun kolin kasar, yayin da Yan Sanda suka sa ido domin kaucewa tashin hankali.

Yayin zanga-zangar a yau gungun lauyoyin sun yi ta ihun cewar su na bukatar Jamhuriya ce ba mulkin mallaka ba.

Kungiyar lauyoyin ta bukaci kafa gwamnatin rikon kwarya da kuma dage zaben da ake shirin yi, wanda tuni shugaba Bouteflika ya gabatar da takardar takara, daga inda ya ke jinya a Switzerland.