Isa ga babban shafi
Najeriya-Enugu

'Yan sanda sun kashe mai sa ido kan zabe a Enugu

'Yan Sanda a Jihar Enugu da ke Tarayyar Najeriya sun tabbatar da kashe wani mai sa ido kan zaben Gwamna da na 'yan Majalisun jiha da aka gudanar yau Asabar.

Akwatin zaben Najeriya
Akwatin zaben Najeriya guardian.ng
Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya jiyo wani dan sanda na tabbatar masa da aukuwar lamarin, wanda ya ce harsashin 'yan Sanda ne ya same shi lokacin da su ke kokarin tarwatsa masu zanga zanga.

Majiyar ta ce masu zanga zangar sun bukaci dage zaben na yau ne, domin bai wa dan takarar Jam’iyyar APC Ayogu Eze damar shiryawa zaben, bayan nasarar da ya samu a kotu.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce akalla mutane 10 aka kashe a zaben da aka gudanar yau a sassan Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.