Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire-Faransa

Tangardar Inji ta tilastawa jirgin Air France saukar gaggawa a Abidjan

Matsalar Inji ta tilastawa wani jirgin saman Air France kirar A380 dauke da fasinjoji sama da 500 sake komawa birnin Abidjan da ke kasar Cote d’Ivoire inda ya sake sauka ba tare da wata matsala ba.

Tuni dai jirgin ya koma birnin Abidjan don duba lafiyarsa kafin daukar hanya zuwa Faransa
Tuni dai jirgin ya koma birnin Abidjan don duba lafiyarsa kafin daukar hanya zuwa Faransa Reuters
Talla

Wani dan jaridar da ke aiki da kamfanin Bloomberg, Baudelaire ya ce su na cikin tafiya Paris a sararin samaniyar Jamhuriyar Nijar, sai ya ga hayaki, daga bisani kuma ya ji kara a gefen hagu na jirgin, sannan jirgin ya fara tangal tangal, mutane kuma suka razana, suna ta addu’oi.

Dan jaridar ya ce daga nan matukin jirgin ya sanar da su cewar, injin da ke gefen hagu ya lalace, saboda haka za su koma Abidjan.

Manajan kamfanin jiragen Air France da KLM da ke kula da Afirka ta Yamma, Jean Luc-Mebellec ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce akan samu irin wannan matsala jifa jifa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.