rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Algeria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaba Bouteflika na Algeria ya bada kai bori ya hau

media
Shugaba Abdelaziz Bouteflika na Algeria RYAD KRAMDI / AFP

Shugaban Kasar Algeria, Abdelaziz Bouteflika ya bada kai bori ya hau, wajen janyewa daga takarar zabe wa’adi na biyar, sakamakon matsin lambar da ya fuskanta wajen zanga zanga daga ciki da wajen kasar.


Sakamakon janye takarar, shugaban ya kuma dage zaben shugaban kasar da aka shirya gudanarwa ranar 18 ga watan Afrilu don bada damar gudanar da taro na kasa da kuma rubutawa kasar sabon kundin tsarin mulki nan da karshen shekarar 2019.

Bouteflika da ke fama da rashin lafiya da yawan shekaru ya koma gida ne ranar lahadi daga Switzerland inda aka duba lafiyar sa.

Tuni mutane kasar suka barke da murna su na kade-kade sakamakon matakin da shugaban ya dauka, bayan kwashe dogon lokaci ana gudanar da zanga zangar adawa da aniyar sa.

A wani labari kuma, shugaba Abdelaziz Bouteflika ya nada ministan cikin gida Bedoui a matsayin sabon Firaminista.