rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Afrika Djibouti Habasha Faransa Emmanuel Macron

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaban Faransa na ziyara a wasu kasashen Afrika

media
Shugaban Faransa Emmanuel Macron, tare da takwaransa na kasar Djibouti, Ismaïl Omar Guelleh. CHRISTOPHE ARCHAMBAULT / AFP

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na ziyara a kasar Habasha a ci gaba da rangadin da ya fara a wasu kasashen Afirka, inda ya sauka a Djibouti da yammacin ranar Litinin 11 ga watan Maris.


Da safiyar yau shugaba Emmanuel Macron ya gana da shugaban Djibouti, Isma’il Omar Guelleh, kuma daga cikin batutuwan da aka sa ran sun tattauna harda halin da ake ciki a Algeria da kuma janye takarar shugaba Abdelaziz Bouteflika, wadda ta raba kan jama’ar kasar.

Daga bisani shugaba Macron zai gana da kwamandan sojin Faransa dake kula da sansanin sojin kasar a Djibouti, wanda shi ne mafi girma a kasashen ketare.

Da tsakar rana, shugaba Macron zai tashi zuwa Lalibela dake da nisan kilomita 680 daga birnin Addis Ababa a kasar Habasha, inda ake da mujami’un da aka gina a karni na 13 wadanda hukumar UNESCO ta sanya su a cikin wuraren tarihi na duniya.

Ana sa ran shugaba Macron ya bayyana wata yarjejeniyar hadin kai tsakanin Faransa da Habasha na kare wuraren wadanda zaizayar kasa ke yiwa barazana.