rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Algeria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan Algeria na ci gaba da bore kan lallai Bouteflika ya yi murabus

media
Ilahirin masu zanga-zangar sun rike kwalaye dauke da rubutu da ke cewa mulkin kasar ba kwallon kafa ba ne da za a kara lokaci REUTERS/Zohra Bensemra

Dubban masu zanga-zanga a Aljeria sun ci gaba da gangamin bukatar shugaba Abdelaziz Boutrflika ya yi murabus, duk da matakin janye batun sake tsayawa takara karo na biyar da shugaban ya yi a jiya.


Daruruwan masu zanga-zangar galibi dalibai sun taru a manyan biranen kasar ta Algeria inda su ke neman lallai shugaban mai shekaru 82 da ke fama da shanyewar barin jiki ya yi murabusa, duk da matakinsa na janye kudirin sake tsayawa takara a karo na biyar.

Ko da dai ana ganin babban abin da ya kara harzuka al’ummar Algeriyan bai wuce batun sauya lokacin zaben kasar da shugaba Bouteflika ya yi ba, wanda a baya aka tsara gudanarwa a wata mai kamawa.

Masu zanga-zangar dai na da ra’ayin cewa shugaba Bouteflika na kokarin wasa da hankalinsu ne wajen karawa kansa wa’adi mai tsayi kafin amincewa da gudanar da babban zaben kasar.

Cikin kalaman shugaba Boutrflika a jiya Litinin, ya ce ba zai tsaya takara a karo na biyar ba, haka zalika babu batun zabe a watan Aprilu, yayinda ya sanar da nadin sabon Firaminista, matakin da ke nuna cewa bai tsayar da ranar sauka daga mulki ba.

Kasar ta Algeria wadda rabin yawan jama’arta matasa ne da shekarunsu bai haura 30 ba, ilahirin masu zanga-zangar sun rike kwalaye dauke da rubutu da ke cewa mulkin kasar ba kwallon kafa ba ne da za a kara lokaci.