rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Lagos

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ana fargabar mutuwar kananan yara bayan ruftawar bene mai hawa 3 a Lagos

media
Jami'an agajin da ke lalubo kananan yaran da suka makale a benen bayan ruguzowarsa yau a Lagos RFI hausa

Rahotanni daga jihar Lagos a Najeriya na cewa akalla kananan yara 10 ake fargabar sun makale a baraguzan gine-gine bayan rugujewar wani gini mai hawa 3 a unguwar Itafaji da ke jihar.


Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar wadda ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce yanzu haka ana ci gaba da aikin ceton kananan yaran da suka makale a ginin.

A cewar Ibrahim Farinloye kakakin yada labaran hukumar agajin gaggawar ya ce makarantar ita ce hawan karshe na ginin benen mai hawa 3, yayinda ake fargabar mutuwar kananan yara.

Rugujewar gine-gine masu tsayi dai ba sabon abu ba ne a Najeriya don ko a watan Satumban 2014 ma akalla mutane 116 ne suka mtu bayan fadowar wani gini mai hawa 6 a jihar ciki har da 'yan kasar Afrika ta kudu 84, wanda daga bisani kuma aka gano cewa an yi ginin ne ba bisa ka'ida ba.

Ka zalika ko a watan Disamban 2016 ma wani ginin Majami'a da ya ruguzo a jihar Uyo da ke kudancin Najeriyar ya hallaka mutane 60.