rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rahotanni Tarayyar Afrika Chadi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An fara bikin baje kolin amfanin gona na nahiyar Afrika a Chadi

media
Wasu mata da ke kasuwar baje kolin a Chadi LA Bagnetto

A Kasar Chadi, yanzu haka an bude wani taron baje kolin amfanin gonar da ake kira Safagri jiya talata. Wannan bikin baje koli da ya ke gudana a tsakiyar birnin Ndjamena zai cigaba da ci har zuwa ranar juma’a.Shi dai wannan biki wata kafa ce da za ta ba da damar tattaunawa da musayar bayanai tsakanin manoma da kwararru domin bunkasa aikin noma a Afirka, wanda aka dade ana bayyana cewar baya samun cigaba.

Mutane sama da 200 daga kasashen Mali da Burkina Faso da Togo da Mauritania ke baje kolin amfanin gonar su. Wannan wata dama ce ta gabatar da amfanin gonar da ake sarrafa shi gaba daya a Afirka.


An fara bikin baje kolin amfanin gona na nahiyar Afrika a Chadi 13/03/2019 - Daga Azima Bashir Aminu Saurare