rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
  • Palestinawa 22 hare-hare daga Israela ya kashe a Gaza.
  • Dan kunar bakin wake ya kashe mutun daya a ofishin 'yan sandan Indonesia

Rwanda Tarayyar Afrika Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rwanda ta gayyaci Emmanuel Macron

media
Paul Kagame, Shugaban kasar Rwanda © AFP

Kasar Rwanda ta gayyaci shugaban Faransa Emmanuel Macron da ya halarci bikin tunawa da mutane sama da 800,000 da aka kashe a kisan kiyashin da ya biyo bayan yakin basasar kasar a shekarar 1994.


Karamin ministan harkokin wajen kasar, Olivier Nduhungirehe yace an gayyaci Macron bikin da za’ayi ranar 7 ga watan gobe, gayyatar dake zuwa a matse.

Rwanda ta dade tana zargin Faransa da goyan bayan gwamnatin Hutu da kuma horar da sojojin ta da yan tawayen su da suka aikata kisan kan yan kabilar Tutsi.

Shugaba Macron da yanzu haka ke ziyarar kasashen Djibouti da Habasha da Kenya bai bayyana ko zai amsa gayyatar ba.