rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kenya Emmanuel Macron Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Macron ya zargi Kabila da yiwa Tshisekedi katsalandan a mulki

media
Shugaba Maron yayin taron muhalli na duniya da ke gudana a kasar Kenya REUTERS/Thomas Mukoya

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, da ke ziyara a yankin gabashin Afrika ya nemi takwaransa na Jamhuriyar Demokradiyar Congo ya dau nauyin da ya rataya a wuyansa tare da kaucewa barin tsohon shugaban kasar Joseph Kabila, na yi masa katsalandan a cinkin harkokin tafiyar da mulkinsa.


A lokacin wata ganawa a Nairobin da shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, shugaban na Faransa Emmanuel Macron ya bukaci takwaransa na Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo Felix Tshisekedi da ya yi kokrin mika hannu ga dan adawa Martin Fayulu, da ya yi ikararin lashe zaben shugabancin kasar na watan December da ya gabata.

Bayan da ya yi nasarar lashe zaben kasar na ranar 30 ga watan Disamban bara, tare da karbar rantsuwa a ranar 24 ga watan Janairun da ya gabata, har zuwa yau tsohon dan adawar, Félix Tshisekedi bai nada Firaminista ko kuma kokarin kafa gwamnati ba, wanda kuma hakan ke da alaka da kawancen siyasar da ya kulla da magabacinsa Joseph Kabila, kawancen da ke rike da mafi yawan kujeru a majalisar dokokin kasar.

A cikin jawabin da ya gabatar na 15 ga watan Fabrairun jiya a gaban Jamián Diflomasiyar kasashen duniya a Kinshasa, Shugaba Tshisekedi ya bukaci Tarayyar Turai ta cire takunkuman da ta kakabawa wasu tsofin shugabanin kasar da suka gabata.

Sai dai a ziyarar sa a Kenya, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci shugaba Tshisekedi da ya dau nauyin da ya rataya a wuyansa tare da nisanta kansa da tsohon shugaban kasar Joseph Kabila.