rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamus Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shirin mayarwa Afrika da kayayyakin tarihi daga Jamus

media
Wasu daga cikin kayan tarihi a gidan kalo na Dakar a Senegal Yasmine Chouaki/RFI

Jamus ta amince da gaggauta aiwatar da shirin maido da muhimman kayayyakin tarihin kasashen nahiyar Afrika, da suka taba kasancewa a karkashin mulkinta, inda a waccan lokacin dakarunta suka yashe yankunan bayan hallaka dubban jama’a.


Ma’aikatun kare al’adu da na harkokin wajen kasar ta Jamus ne suka jagoranci rattaba hannu kan kudurin, tare baiwa gidajen adana kayan tarihi da cibiyoyin kimiyya da ke kasar, umarnin soma kidaya da tattance kayayyakin tarihin da aka ajiye tare da su a zamanin mulkin mallaka.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da Jamus ke wannnan kokari ba, domin a shekarun baya bayan nan, ta sha maidawa kasar Namibia muhimman kayan tarihin da dakarunta suka sace, a tsakanin shekarun 1904 zuwa 1908, lokacin da suka yiwa ‘yan kabilun Nama da Herero kisan kiyashi.