Isa ga babban shafi
Nijar

An gano allurar jabu a Nijar

A Jamhuriyar Nijar ,hukumomin sun gano wani nauyin allurar hana kamuwa da cutar sankarau na jabu da yanzu haka ake samu a wasu wurraren sayar da magunguna a Birnin Yameh.

allurar rigakafin kamuwa da cutar sankararau
allurar rigakafin kamuwa da cutar sankararau africa-online.com
Talla

Ministan kiwo lafiya a wata sanarwa da ya sanyawa hannu ya na mai kira zuwa jami’an kiwon lafiya da suyi hatara tareda kira zuwa al’uma don ganin sun tseguntawa jami’an tsaro irin wurraren da ake sayar da wadanan allurai na jabu.

Ranar alhamis da ta gabata dai ne a yayin wani bincike daga jami’an kiwon lafiya na birnin Yameh a wanin shagon sayar da magunguna suka tayar da wannan launin allura, wanda ake zaton shine ya haddasa mutuwar mutane kusan 500 a shekara ta 2015 da wasu 200 a shekara ta 2017 a lokacin da cutar ta kuno kai a wasu sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.