Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

Tsishekedi ya hana sabuwar majalisa soma aiki

Shugaban Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo Felix Tshisekedi, ya hana sabuwar majalisar dattawan kasar fara aiki a jiya, inda ya bukaci a kaddamar da bincike dangane zargin rashawa da ya dabaibaye yadda aka zabe ‘yan majalisar.

Shugaban Jamhuriyar Congo Felix Tshisekedi.
Shugaban Jamhuriyar Congo Felix Tshisekedi. JOHN WESSELS / AFP
Talla

Mukaddashin ministan cikin gidan kasar Basile Olongo, shi ne ya bayar da wannan umarni, bayan da magoya bayan Tshisekedi suka yi zargin cewa jam’iyyar tsohon shugaban kasar ta Joseph Kabila ta lashe mafi yawan kujerun majalisar ne ta hanyar ba da rashawa.

A ranar 26 ga watan Maris da muke ciki majalisar dattijan ta Jamhuriyar Congo ta tsara kaddamar da bincike kan zargin aikata Rashawar, amma yanzu aka dage har zuwa wani llokaci nan gaba da ba’a bayyana ba.

A gefe guda shugaba Tshisekedi ya kuma bukaci lauyoyin gwamnati, su soma bincike kan zarge-zargen cin hanci da Rashawa da ake yiwa ministoci da sauran manyan mukarraban gwamnatin Joseph Kabila.

A makon da ya gabata, sabon shugaban Jamhuriyar Congo Felix Tshisekedi, ya yi afuwa ga yan adawa da dama, hadi da ‘ya’yan kungiyar fararen hula da gwamnatin tsohon shugaba Joseph Kabila ya daure.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.