rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Algeria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jam'iyyun siyasar Algeria sun janye goyon baya ga Bouteflika

media
Shugaban kasar Algeria Abdelaziz Bouteflika ©REUTERS/Ramzi Boudina/File Photo

Wata Babbar Jam’iyyar siyasa a Algeria da ake kira ‘National Rally for Democracy’ da ke goyan bayan shugaba Abdelaziz Bouteflika ta cacaki matakin shugaban na ci gaba da zama a karagar mulki bayan kammala wa’adin sa a watan gobe, matakin da ake ganin sa a matsayin babbar koma baya ga gwamnati.


Jam’iyyar ta RND ta bi sahun Jam’iyyun kawance da kungiyoyin kwadago da 'yan kasuwa da suka daina goyan bayan shugaban mai fama da rashin lafiya.

Kakakin Jam’iyyar, Sedik Chihab ya bayyana cewar aniyar sake takarar shugaba Bouteflika babban kuskure ne.

Shi ma shugaban Jam’iyyar RND Ahmed Ouyahia, wanda tsohon Firaminista ne, ya janye goyan bayan shugaban.