rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ghana Togo Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mutane 60 sun mutu sakamakon hadarin mota a Ghana

media
Hadarin motocin bas Ghana, 22 Sept 2019 Ghana.news

Akalla mutane 60 ne suka rasa rayukansu sakamakon hadarin da wasu motocin daukar fasinja biyu suka yi yankin Bono da ke kudu maso gabashin kasar Ghana.


Mai magana da yawun ‘yan sandan kasar ta Ghana Joseph Antwi Gyawu, ya ce motocin sun yi taho mu-gama ne da misalin karfe biyu na daren da ya gabata.

Bayanai sun ce bayan da motocin suka yi taho mu-gama, nan take daya daga cikinsu ta kama da wuta, a lokacin kowace mota na dauke da fasinjoji  50 a cikinta.

Kwame Arhin, likita a asibitin gwamnati da ke garin Kintampo kusa da inda lamarin ya faru, ya ce yanzu haka akwai mutane 28 da aka kwantar a asibitin don kula da su sakamakon raunukan da suka samu.

A shekara ta 2016, wata motar fasinja ta yi taho mu gama da wata motar daukar kaya a kan hanyar Tamale, inda mutane 53 suka rasa rayukansu