rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Chadi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Boko Haram, ta kashe sojin Chadi 23 tare da fararen hula 8 a Nijer

media
A Chadian soldier poses for a picture at the front line during battle against insurgent group Boko Haram in Gambaru, February 26, 2015. REUTERS/Emmanuel Braun REUTERS/Emmanuel Braun

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai wani sabon hari a cikin daren jiya alhamis kawo safiyar yau juma’a, inda suka kashe sojojin Tchadi 23 tare da fararen hula 8 a jamhuriyar Nijer, kamar yadda majiyoyin kasashen Tchadi da Niger suka tabbatar.Rundunar sojin Tchadi da yi zufa a sakamakon wannan hari da ya kasance mafi daukar rayukan a a yakin da take yi da mayakan jihadin na Boko Haram, ta ce an kai mata harin ne a sansaninta dake Dangdala, kudu maso yammacin kasar ta Tchadi.


Wata majiya ta sanar da kamfanin dillancin labaran AFP, cewa, da misalin karfe 1 dare jiya lahamis ne, mayakan na Boko Haram suka kai wa sansanin sojin na Chadi hari, inda suka kashe sojoji 23

Maharan na Boko Haram sun fito ne daga jamhuriyar Nijer, kafin kai harin kan sansani sojan na Chadi dake da gabar arewa maso gabashin tafkin Chadi. Majiyar ta kara da cewa, mayakan na Boko Haram sun yi nasarar arcewa da makamai da kuma albarusai masu tarin yawa.

Sojan Tchadi dake cikin rundunar dakarun hadin guiwa ta (FMM) mai yaki yakar kungiyar jihadin ta Boko Haram, da a 2015 ta fara kai hare haren a cikin kasar ta Chadi.

Har ila yau, mayakan Jihadin na Najeriya sun kai hari a jamhuriyar Niger mai makwabtaka, inda ajiya alhamis suka kashe fararen hula 8, a garin Gueskerou, dake kudu maso gabashin kasar, daf da kan iyakarta da tarayyar Najeriya

Yanzu haka dai, hare haren na yan Boko Haram sun zama ruwan dare a yankin Diffa, dake gabar tafkin Chadi, da ya zama gijen mayakan dake ikararin jihadi a Najeriya, tafkin da ya hada kasashen Nijer, Najeriya da kuma Chadi.

A ranar 9 ga watan Maris, sojojin gwamnatin Nijer 9 ne suka rasa rayukansu karkashin wani harin da kungiyar ta Boko Haram ta kai a wani wuri dake kusa da garin Gueskerou na jihar Diffa.

A ranar 16 ga watan Fabrairu, sojoji 7 Boko Haram ta kashe a wani hari da ta kai a Shétima Wangou, wani kauye dake kusa da kan iyakar Nijer da Najeriya.

Rundunar sojan Nijer da ta kara rubanya kai farmakinta, ta yi nasarar kashe yan Boko Haram 33 a ranar 12 ga watan Maris, a wani babban samame da ta kai, tare da kwato mota mai silke, da kuma makamai da albarusai masu tarin yawa da ga hannu yan ta’adan.

A karshe 2018, rundunar sojan ta Nijer ta bayyana kashe yan taddan kungiyar Boko Haram 200 a wani gagarumin hari da ta kai ta kasa da sama. To sai dai mahukumtan Yamai, sun ce duk da haka, har yanzu lamuran tsaro basu inganta ba a wannan yanki na Diffa, al’amarin da yasa a farkon wannan mako ta sake tsawaita dokar ta bacin da ta kafa tun cikin 2015 a yankin.

Kungiyar Boko Haram dake da asali daga tarayyar Najeriya, na kai hare hare a ko ina cikin kasashen dake yankin tafkin Chadi da suka hada da (Nigeria, Chadi, Kamaru, da kuma Nijer), inda suke kai munanan hare haren da ke haifar da hasarar rayuka kan jami’an tsaro, tare da yin garkuwa da fararen hula suna karbar fansa

Sama da mutane dubu 27 ne suka mutu, tun farkon barkewar yakin na Boko Haram a 2009, daga yankin arewa maso gabashin Najeriya, tare da tilasta wa kimanin mutane miliyan 1, da dubu 800 barin gidajensu.