rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rwanda Burundi Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Macron ba zai halarci taron juyayin kisan kiyashin Rwanda ba

media
Kasusuwan mutnen da aka hallaka a kisan kiyashin Rwanda Reuters

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ba zai halarci taruruka da addu’o’in cika sekaru 25 da barkewar kisan kiyashin kasar Rwanda da za a yi ranar 7 ga watan afrilu mai zuwa ba.


Sakamakon kusancin da aka samu tsakanin Faransa da Rwanda bayan zuwan Macron karagar mulki, wannan ya sa gwamnatin Rwanda aike wa shugaban da goron gayyata domin ya halarci wadannan adu’o’I da za a yi a birnin Kigali, to sai Macron ya ce zai tura wani dan majalisar dokokin kasar mai suna Hervé Berville domin ya wakilce shi.

Hervé Berville maraya ne da ya tsira daga kisan kiyashin da aka yi 1994, kafin dauke shi zuwa Faransa lokacin yana da shekaru 4 a duniya.

Shugaban Rwanda Paul Kagame ya share tsawon shekaru yana takun-saka da mahukuntan Faransa, bisa zargin cewa suna da hannu a wannan rikici da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 800 mafi yawansu ‘yan kabilar Tutsi marasa rinjaye a kasar.