rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Mozambique Canjin Yanayi Muhalli Zimbabwe Malawi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Adadin wadanda ambaliya ta hallaka a Mozambique ya karu

media
Wani yankin kasar Mozambique da ambaliya ta mamaye, sakamakon guguwar Idai da ta afkawa kasar. REUTERS/Siphiwe Sibeko

Ana ci ga da samun karuwar wadanda suka hallaka a sakamakon Iftila’in guguwa da ambaliyar da aya afkawa yankin kudancin Afrika.


A kasar Mozambique wadda iftila’in yafi shafa, yawan mutanen da suka hallaka ya karu daga 417 zuwa 446, sai kuma sama damutane dubu 600 da guguwar ta tagayyara.

A makon da ya gabata guguwar a aka yiwa lakabi da Idai ta afkawa garin Biera na Mozambique da ke gabar teku, cikin gudun kilomita 170 a Sa’a guda, daga nan kuma guguwar ta afkawa Zimbabwe da kuma Malawi inda a nan ma ta tafka barna.

A Zimbabwe mutane 259 suka hallaka a iftila’in guguwar da ambaliyar, wasu 200 suka jikkata, yayinda mutane dubu 16 suka rasa muhallansu.

A Malawi kuwa mutane 56 suka mutu, wadanda mafi akasari suka hallaka a dalilin mamakon ruwan sama babu kakkautawa, gabannin isowar guguwar, wasu 577 kuma suka jikkata, sai kuma mutane dubu 94 da suka rasa muhallansu.