Isa ga babban shafi
Afrika-Duniya

Fafaroma Francis ya gana da Sarki Mohammed na Morocco

A yau asabar Shugaban darikar Katolikan ta Duniya Fafaroma Francis ya kaddamar da wata ziyara zuwa kasar Morocco, indan ya samu tattaunawa da Sarkin Morocco Sarki Mohammed na Shida wanda ya gayyace zuwa Morocco.

Fafaroma Francis tareda rakiyar Sarkin Morocco Mohammed na shida
Fafaroma Francis tareda rakiyar Sarkin Morocco Mohammed na shida FADEL SENNA / AFP
Talla

Akala mutane dubu 25 ne ake sa ran za su tarbi Fafaroma Francis da kuma kasancewa a muhimin wurin da zai gabatar da jawabi zuwa magoya bayan sa.

Daga cikin batutuwan da ake sa ran Fafaroma ya tattauna da Sarki Mohammed na shida sun hada da cimma zaman lafiya ta hanyar musulunci da kuma batun bakin haure dake ci gaba da rasa rayukan su a kokarin tsallakawa zuwa Turai ta hanyar teku.

A daya Geffen hukumomin Morocco sun sanar da cimma wani sabon tsari na wayewa matasa kawunan su dangane da batutuwa da suka shafi adinin musulunci.

wata makaranta dake samun hadin gwuiwa daga wasu kasashen Afrika ta kaddamar da wani shiri na bayar da horo zuwa dalibai dangane da hanyoyin samar da zaman lafiya tareda yin amfani da ilimin dake cikin alkur’ani.

Tattaunawa,cima sulhu da kuma yin amfani da adinin musuluncin domin cimma wadanan muradu ,na daga cikin hanyoyin da wannan jami’a da aka yiwa sunan Makarantar Mohammed na shida dake bayar da horo zuwa daliban kasashen Mali, Cote D’ivoire, Guinee Conakry, Sanegal, Chadi, Najeriya, Gambiya da Faransa ta saka a gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.