Isa ga babban shafi
Gambia

Jammeh ya sace sama da dala miliyan 350 - Rahoto

Ministan Shari’ar Gambia Abubakar Tambadou, yace tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh, ya sace dala miliyan 362 a tsawon shekaru 22 da ya shafe yana mulki.

Tsohon shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh.
Tsohon shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh. MARCO LONGARI / AFP
Talla

Ministan shari’ar na Gambia ya ce an bankado badakalar ce, bayan shafe shekaru 2 ana gudanar da bincike kan Gwamnatin Jammeh, inda suka gana da shaidu 253.

Jammeh wanda ya soma mulkin Gambia a shekarar 1994 bayan yin juyin mulki, ya koma gudun hijira a Equatorial Guinea cikin shekarar 2017, bayan shan kaye a zaben shugabancin kasar da Adama Barrow yayi nasara, wanda a waccan lokacin sai da aka yi barazanar amfani da karfin soja wajen tilasta masa sauka kafin ya mika mulkin.

Har yanzu dai Jammeh bai ce komai ba kan rahoton, sai dai magoya bayansa da ke Gambia sun yi watsi da binciken, da suka bayyana a matsayin bita da kulli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.