rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Ebola WHO Lafiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Cutar Ebola na sake yaduwa cikin gaggawa

media
Ma'aikatan kiwon lafiya da ke aikin kawar da cutar Ebola Photo: John Wessels/AFP

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta bayyana cewa, cutar Ebola na ci gaba yaduwa cikin gaggawar da ba a taba ganin irinta ba, bayan watanni takwas da sake barkewarta a Jamhuriyar Demokradiyar Congo.


Dimbin jama’a ne suka kamu da cutar a cikn makwanni biyu da suka gabata, abinda ke haifar da koma-baya wajen yaki da ita, yayinda kuma rikicin ‘yan tawaye ya hana jami’an kiwon lafiya isa yankunan da ibtila’in ya shafa.

WHO ta bayyana cewa, yawan wadanda suka kamu da cutar a makwanni biyu da suka shude sun kai 129, in da a makon farko aka samu mutane 57, yayinda a mako na biyu aka samu mutane 72 kamar yadda Christian Lindmeier, mai magana da yawun WHO din ta bayyana.

Lindmeier ta ce, mutana na ci gaba da kamuwa da cutar ba tare da daukan matakan kariya ba.

A halin yanzu dai, cutar ta kashe mutane 676, yayinda 406 suka kamu da ita, in da kuma 331 suka yi katarin warkewa daga annubar.