Isa ga babban shafi
Algeria

Shugaban kasar Algeria yayi murabus

Rahotanni daga Algeria sun tabbatar da cewa shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika yayi murabus, jim kadan bayan umarnin da rundunar sojojin kasar ta bada na soma aiwatar da shirin tsige shugaban.

Shugaban Algeria Abdelaziz Bouteflika tare da babban Hafsan sojin kasar Ahmed Gaid Salah a birnin Algiers.
Shugaban Algeria Abdelaziz Bouteflika tare da babban Hafsan sojin kasar Ahmed Gaid Salah a birnin Algiers. REUTERS/Ramzi Boudina
Talla

Shugaban sojojin Algeria, Janar Ahmad Gaid Salah ne ya bada umarnin, cikin wata sanarwa da ma’aikatar tsaron kasar ta fitar a wannan Talata.

Sai dai cikin yanayi na bazata labarin murabus din shugaba Bouteflika ya bayyana, bayan shafe makwanni da dama dubban 'yan Algeria na gudanar da zanga-zangar neman kawo karshen mulkinsa na tsawon shekaru 20.

Umarnin ya zo ne kwana guda bayan da fadar gwamnatin Algeria ta bayyana cewa shugaba Bouteflika ya amince zai yi murabus kafin ranar 28 ga watan Afrilu.

Sai dai rundunar sojin kasar ta Algeria ta yi watsi da alkawarin, tare da bayyana shi a matsayin na bogi, la’akari da cewa, ba shugaba Bouteflika bane ya furta hakan da bakinsa.

A ranar Litinin fadar gwamnatin Algeria ta ce shugaban kasar AbdelAziz Bouteflika zai yi murabus kafin ranar 28 ga watan Afrilu, lokacin da wa’adinsa zai kare.

Cikin sanarwar da ta fitar fadar gwamnatin ta ce shugaba Bouteflika mai shekaru 82 zai sauka ne bayan daukar wasu muhimman matakai, wadanda ba a bayyana ba.

Matsin lambar tilastawa Bouteflika yin murabus ya soma ne bayanda shugaban ya bayyana aniyar neman wa’adi na 5 a babban zaben kasar da a baya aka tsara zai gudana a ranar 18 ga watan Afrilu.

Bayan zafafar zanga-zangar dubban ‘yan Algeria, Bouteflika ya janye aniyarsa ta neman tazarce, amma da sharadin dage zabukan kasar zuwa wani lokaci da bai bayyana ba.

Matakin shugaban na Algeria ya sake tunzara masu zanga-zangar wadda dubban dalibai da malamansu da kuma manyan lauyoyi suka shiga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.